Accessibility links

Rikicin Manoma Da Makiyaya Na Iya Haddasa Karancin Abinci A Najeriya


Wasu makiyaya na kallon ramammun dabbobin su, na kalace-kalacen abinci a kasa a wata kasuwar Dakoro a kasar jamahuriyar Nijer.

Shugaban Kwamitin Sake Shata Burtalolin Shanu, Gwamna Murtala Nyako, Yace Tilas A Gaggauta Shinge Sauran Wuraren Kiwon Da Suka Rage

Gwamnati a Najeriya ta ce jihohi 17 a sassa dabam-dabam na kasar ne suke fuskantar tashe-tashen hankula a tsakanin Fulani makiyaya da manoma na wadannan jihohi a saboda rikici kan wurin kiwo.

Haka kuma an ce wasu masu munanan manufofi suna fakewa da wadannan tashe-tashen hankula domin gudanar da aika-aikarsu.

A dalilin wannan yasa majalisar tattalin arziki ta Najeriya ta kafa Kwamiti karkashin jagorancin gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa, domin shata burtalolin shanu inda makiyayan suke kiwo da shanunsu.

A cikin wata hira da sashen Hausa, gwamnan ya roki sassan biyu da su kai zuciya nesa. Yace a yanzu, jama’a sun yi gine-gine, ko kuma sun yi gonaki a kan burtalolin da tun faro aka ware domin shanu da masu kiwonsu, ahinda shi ne ke rura wutar wannan fitina.

Gwamna Nyako ya roki jihohi da su gaggauta yin shinge su kewaye sauran burtalolin da suka rage a jihohinsu domin jan burki ma wannan tashin hankalin.

Shugabannin kungiuyoyin makiyaya kamar na Miyeti Allah da suka tattauna da wakilinmu sun ce har yanzu ana kai hare-haren sari ka noke a kan makiyaya ana sace musu shanu tare da kasha wasunsu.

Ga cikakken rahoto da bayanin na wakilinmu nan.
XS
SM
MD
LG