Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Nijar Ya Kara Zafafa Matsalar Karancin Abinci a Kasar-Majalisar Dinkin Duniya


 ‘Yan Nijar Na Tayin Kafa Rundunar ‘Yan Sa- Kai Don Tallafawa Dakarun Kasar
‘Yan Nijar Na Tayin Kafa Rundunar ‘Yan Sa- Kai Don Tallafawa Dakarun Kasar

A jiya laraba, MDD tayi gargadin cewa, rikicin dake cigaba da faruwa a kasar Nijar, na iya kara ta’azzara matsalar karancin abinci a kasar, inda ta bukaci a tsame ayyukan jinkai da rufe kan iyakoki, daga takunkumin da aka aza, domin kaucema afkuwar bala’i

Hukumar ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, ko kafin ayi juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Shugaba Muhammed Bazoum, a karshen watan jiya, kasar ta kiyasta mutanen dake fuskantar matsanancin karancin abinci sama da milyan 3.

Haka kuma mutane sama da milyan 7 da aka dauka a matsayin masu dan dama dama, ga matsalar abincin, a yanzu lamarin su Ka iya baci, sakamakon rikicin da ya kunno kai, kamar yadda hukumar kula da ayyukan jinkan ta Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadi, inda ta yi misali da bayanan Hukumar abinci ta Majalisar.

A ranar 26 ga watan Yuli ne dai wasu dakarun tsaron Shugaban kasa, suka tsare Bazoum mai shekaru 63 a duniya, a juyin mulki na 5 da aka yi a kasar Nijar tun bayan samun ‘yancin kanta daga Faransa, a shekarar 1960.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace, tana cigaba da kai taimakon abinci cikin Nijar, duk kuwa da rikicin siyasar dake cigaba da rarakar kasar mai fama da talauci.

A halin da ake ciki kuma, yau Laraba Amurka tace,tana cigaba da bibiyar abin dake faruwa a kasar. Ta ce, Sabuwar Jakadiyar ta a Nijar, Kathleen Gibbon, zata isa birnin Yamai, duk kuwa da juyin mulkin da aka yi a kasar a watan jiya.

Wani jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Amurka yace, ana sa ran isarta Nijar a wani lokacin cikin mako mai zuwa.

A karshen watan jiya ne, jim kadan bayan juyin mulkin, Majalisar Dattawan Amurka ta amince da nadin Kathleen, wadda jami’ar diplomasiyya ce a harkokin kasashen waje, kusan shekara guda da zabarta a mikamin.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken

Mataimakin mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Vedant Petel ya shaidawa manema labarai cewa, ba wani shirin da aka yi na ta mika takardun ta ga jagororin juyin mulkin, kuma aikin da za ta yi a ofishin jakadancin baya bukatar hakan.

Ya kara da cewa, zata tafi can ne domin jagorantar ofishin jakadancin a yanayi mai wahala, domin mara baya ga alummar Amurkawa, da kula da kokarin da gwamnatin Amurka ke yi.

Duba Tarihin Juyin Mulki A Jamhuriyar Nijar Tun Bayan Samun 'Yancin Kai
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00

~Hauwa Sheriff~

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG