Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin PDP: Walid Jibrin Ya Yi Murabus Daga Mukamin Shugaban Kwamitin Amintattu, An Nada Wabara


Walid Jibrin (Hoto: Channels)
Walid Jibrin (Hoto: Channels)

A kwanakin baya, rahotanni sun yi nuni da cewa Walid Jibrin da kansa ya fito ya ce bai dace a ce dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyya su fito daga yanki daya ba.

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa, Shugaban Kwamitin Amintattu na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Sanata Walid Jibrin ya yi murbaus daga mukaminsa.

Bayanai sun yi nuni da cewa, Jibrin ya yi murabus ne, a wani mataki na yayyafa ruwan sanyi kan rikicin shugabanci da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawar.

Gwamna Ifeanyi Okowo, hagu da Atiku Abubakar, dama (Hoto: Facebook/Ifeanyi Okowo)
Gwamna Ifeanyi Okowo, hagu da Atiku Abubakar, dama (Hoto: Facebook/Ifeanyi Okowo)

“Zan sauka daga mukamina a matsayin shugaban kwamitin amintattu saboda na sawwaka kowa.” Jibrin ya fada a wajen taron kwamitin zartwar jam’iyyar da ke gudana a Abuja a ranar Alhamis, kamar yadda Channels ya ruwaito.

A halin da ake ciki, annada tsohon shugaban Majalisar Dattawa Adolphus Wabara a matsayin shugaban kwamitin don maye gurbin Jibrin

Gabanin ba shi wannan mukami, Wabara shi ne Sakataren kwamitin.

Jam’iyyar ta PDP ta tsinci kanta a cikin rikicin shugabanci tun bayan da ta yi babban taronta na kasa da ya zabi Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasar.

Gwamna Nyesom Ezenwo Wike na jihar Ribasa.
Gwamna Nyesom Ezenwo Wike na jihar Ribasa.

Bayan da aka zabi gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa, gwamnan Rivers, Nyesom Wike yake kalubalantar yadda dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyya suka fito daga yankin arewacin Najeriya.

Hakan ya sa Wike da magoya bayansa, suka nemi shugaban jam’iyya Dr. Ayu Iyorchia da ya yi murabus, suna masu nuni da cewa akwai yarjejeniya da ta amince cewa, Ayu ya amince zai yi murabus idan dan takarar shugaban kasa ya fito daga arewaci.

Shugaban jam'iyyar PDP, Dr. Iyorchia Ayu
Shugaban jam'iyyar PDP, Dr. Iyorchia Ayu

Ko a kwanakin baya,Jibrin da kansa ya yi nuni da cewa bai dace a ce dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyya su fito daga yanki daya ba.

Shi dai Ayu ya ce, ba zai sauka ba har sai wa’adin shekaru hudu da doka ta tanada masa ya kare.

XS
SM
MD
LG