Accessibility links

Rikicin PDP an dauka zai taimakawa jam'iyyar APC to amma sai gashi PDP na cigaba da cin zabe a kudu maso yammacin kasar da kudancin kudu.

Yayin da rikicin PDP ya barke ana zaton zai taimakawa sabuwar jam'iyyar APC to ko akwai alamar hakan yana faruwa?

Rikicin PDP da ya barke ya sa jam'iyyar APC ta yi shiri cikin tsanaki domin kwace madafin iko daga PDP a shekarar 2015 maimakon fafe gorar tafiya. To amma shugaban PDP Alhaji Bamanga Tukur ya ce rikicin ya lafa. Duk da ikirarin Bamanga Tukur bai hana sabuwar PDP daukaka kara ba bisa ga nasarar da wata kotu ta baiwa bangaren tsohuwar PDP. Bugu da kari sabuwar PDP tana cigaba da nada shugabanni a jihohin Najeriya.

Mataimakin kakakin jam'iyyar PDP Barrister Abdullahi Jalo ya ce bai ga wata jam'iyyar adawa da zata iya karbe madafin iko daga hannun PDP ba. Ya ce wane rikici PDP ta shiga har ana maganar tureta. Ya ce kwanan nan aka yi zabe a jihohin Ondo da Ekiti duk PDP ta lashe. Wadanda ake zaton zasu sha gaban PDP suna ciki aka yi zabe. A jihar Kogi ma PDP ta ci zaben kananan hukumomi. Ya ce duk inda aka yi zabe PDP na lashewa duk da rashin fahimta da ta faru tsakinsu da wasu masoyansu domin manya ne a jam'iyyar. Ya ce abun da ya faru shi ne idan dambu ya yi yawa baya jin mai to amma an samu wanda zai sa mai da yawa wato Bamanga Tukur.

Ita ma 'yar kwamitin amintattu na PDP Christie Silas ta yiwa APC gatse. Ta ce APC ai maganin ciwon kai ne kuma an daina shanshi. Yanzu panado ake sha. An manta da APC. Babu mai yayin APC sai dai PDP. Ta ce duk dan Najeriya mai son cigaban kasar, mai son hadin kai dole ya bi jam'iyyar PDP.

Wani jigo a matasan jam'iyyar APC a jihar Gombe kuma wanda yake son tsayawa takara a shekarar 2015 ya ce sun daura damarar kawar da PDP a jihar. Ya ce suna son mutane su bar jam'iyyar da ta kwashe shekaru 14 tana kashe mutane tana zaluntarsu. Duk mai son cigaba ya zo ya shiga tafiyarsu ta APC.

Ga karin bayani.


LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”
XS
SM
MD
LG