Accessibility links

Bayan Hukumar Zaben Najeriya ta ki amincewa da sabuwar PDP to ko ina wannan bangaren na Kawu Baraje ya nufa yanzu?

Kwanan nan hukumar zaben Najeriya INEC ta ki ta amince da sabuwar PDP. Haka ma wani kotun tarayya ya yi watsi da karar da suka shigar inda suka nemi a haramtawa Bamanga Tukur shugabancin jam'iyyar.

Cikin wannan lamarin wai ina ita sabuwar PDP ta sa gaba? Da alamu babu sauki a dambarwar siyasar jam'iyyar musamman ma su gwamnonin da suka yi tawaye domin yanzu sun soma barazanar canza sheka. Ana cewa sun soma tuntubar jam'iyyar APC wadda a da can ta ki amincewa da sharudan da wadannan gwamnonin suka shimfida mata kafin su shiga jam'iyyar.

Gwamnan jihar Adamawa ya ce kura fa ta fara ketara bango. Ya fada haka ne yayin da yake karbar tawagar jam'iyyar APC reshen Arewa Maso Gabashin kasar a ofishinsa. Ya ce tun da kura ta fara ketara bango to fa zasu canza tafiya. Ya ce sun datse masu PDP biyu bayan jam'iyyar tana zaune lami lafiya tana cin zabe yadda ya kamata. Ya ce haka kurum aka fada masu har sai da jam'iyyar ta rabu gida biyu. To amma duk da barazanar canza tafiya gwamnan Adamawa Murtala Nyako, daya daga cikin gwamnoni bakwai da suka yi tawaye ya ce shi bai bar PDP ba. Ya ce dole ne irinsu su yi hakuri. Idan ma zata mutu ta mutu a hannunsu. Ya ce har yanzu suna magana da manya ko akwai yadda za'a yi a gyara lamarin domin kada komi ya baci gaba daya.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG