Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Isra'ila Da Falasdinawa:-An Mutane Shida A Gaza


Wani Ba Falasdine yake jifa da duwatsu.

Yanzu rikicin ya kai Gaza inda masu zanga zanga suka tunkari sojojin Isra'ila akan iyaka.

Tarzoma tsakanin Isra'ila da Falasdinawa na tsawon mako daya yanzu ya bazu zuwa zirin Gaza a jiya jumma'a, har sojojin na Isra'ila suka kashe mutane shida a rikicin da aka yi akan iyakokinsu, lamari da ya sa kungiyar Hamas ta nemi jama'a su fito domin a yi karin zanga zanga.

Daruruwan Falasdinawa ne suka nufi ta kan iyakar suna jifa da duwatsu, suna mirgina tayoyi da suka cunnawa wuta zuwa ta kan sojojin Isra'ila da suke gadin kan iyakar. Isra'ila tace sojojinta sun bude wuta ne kan masu hura wutar rikicin, domin dakatar da su daga kaiwa inda suke.

Jami'n kiwon lafiya a yankin Falasidnu suka ce akalla wasu mutane 50 sun jikkata.
An kira zanga zagogin ne domin nuna goyon bayan ga Falasdinawa a birnin kudus da kuma yammacin kogin Jordan, bayan da Falasdinawa suka yi ta daba yahudawa a wukake.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG