Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Robert Mugabe, Tsohon Shugaban Kasar Zimbabwe Ya Rasu.


Robert Mugabe
Robert Mugabe

Emmerson Mnangagwa, shugaban kasar mai ci yanzu ya sanar da rasuwar magabacinsa a sakon da ya kafa a shafinsa na twitter.

Mugabe, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da tara a duniya, ya shugabanci Zimbabwe na tsawon shekaru talatin da bakwai, daga shekara ta dubu da dari tara da tamanin lokacin da kasar ta sami ‘yancin kai daga Birtaniya.

Rundunar soji ta tilastawa Mugabe sauka daga karagar mulki a shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai.

Da farko an rika yabawa Mugabe a matsayin wanda ya kwaci ‘yancin kasar. Sai dai bayan ‘yan shekaru aka shiga kushewa mashi sabili da keta hakkin bil’adama da ya hada da lakadawa ‘yan hamayya duka, da gasa masu akuba da kuma kashe su.

Kasashen yammaci sun kakabawa Mugabe da mukarrabansa takunkumi bayanda magoya bayansa suka fara kwace gonakin fararen fata a shekara ta dubu biyu. Albarkatun gona da ake nomawa a Zimbabwe sun ragu ainun bayanda aka maida gonakin a hannun bakaken fata da basu da kwarewa a fannin noman zamani.

An tsananta kushewa gwamnatinsa a shekara ta dubu biyu da takwas, bayanda tashin gwauron zabi da kayan masarufin suka yi ya kai kashi miliyan dari biyu da talatin da daya cikin dari, abinda ya tilasa kasar Zimbabwe watsi da kudin ta, Dalar Zimbabwe.

Jam’iyar African National Congress ta fitar da sanarwa inda ta bayyana jimamin rasuwar Mugabe wanda tace ya rasu, “bayan ya bautawa kasarsa da kuma al’ummar kasar iya rayuwarsa.”

Sanarwar ta kara da cewa, rayuwar Mugabe manuniya ce ta irin kishin da yake da shi na ganin ci gaban nahiyar, wanda ya fitar da kasar daga danniyar mulkin mallaka ya yi tsayin daka wajen ganin kimar kasar a idanun duniya da kuma ganin kasar ta shata makomarta.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG