Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Robert Mugabe Ya Yi Kiran Hadin Kai a Kasar


Shugaban Kasar Zambabwe Robert Mugabe
Shugaban Kasar Zambabwe Robert Mugabe

Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe, ya yi kiran hadin kai a kasar tare da neman a kawo karshen zanga zangar nuna kyamar gwamnatinsa.

A yau Litinin, Mugabe mai shekaru 92 ya yi wannan kira a wani taro da aka shirya domin karrama tsoffin dakarun da suka kwatarwa kasar ‘yan ci, a wani dandali da ke Harare.

Mugabe ya ce “Ina kira da mu zauna lafiya mu kuma hada kanmu mu ‘yan Zimbabwe, mu kwan da sanin cewa idan babu hadin kai a tsakaninmu ba za mu samu ci gab aba, za a samu rarrabuwar kawuna da fada da tarzoma a tsakaninmu, dalilin haka ya san a ke ganin zanga zanga ba it ace mafitar kasar nan ba, domin ta kan haifar da tarzoma.”

Shi dai Mugabe na fuskantar matsain lamba akan cewa ya sauka daga mukaminsa na shugaban kasa, wanda ya kwashe shekaru 36.

Tattalin arzikin kuma a yanzu haka ya shiga wani mawuyacin hali, bayan matsalar fari da karancin kudi da ya sa ba a iya biyan ma’akata.

A wannan makon da aka shiga ne kuma ake sa ran za samu karin zanga zangar, yayin da gwamnatin ke shirin tsaurara matakan shiga da kayayyaki zuwa kasar daga kasashen waje.

XS
SM
MD
LG