Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ronaldo Ya Musanta Rahotannin Da Ke Cewa Zai Koma Real Madrid


Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo

A ranar Litinin, rahotanni daga Sifaniya sun bayyana cewa dan wasan wanda dan asalin kasar Portugal ne, na shirin komawa Real Madrid da ya baro a 2018.

Dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo ya musanta rahotannin da ake ta yadawa cewa zai koma Real Madrid.

A shekarar 2018 Ronaldo dan shekara 36 ya bar Real ya koma Juventus a gasar Seria A ta kasar Italiya.

A ranar Litinin, rahotanni daga Sifaniya sun bayyana cewa dan wasan wanda dan asalin kasar Portugal ne, na shirin komawa inda ya fito, batun da Ronaldon ya ce babu kamshin gaskiya a ciki.

“Dangane da abin da ake ta fada da rubutawa a kwananan, ya zama dole na fito na bayyana matsayata. Yadda ake yada batun makomata a kafafen watsa labarai ya nuna rashin girmamawa ga dukkan kungiyoyin da ake ambata a wannan labarin kanzon kuregen.” Ronaldo ya wallafa a shafinsa na Instagram, hade da wani hoto da ke nuna alamun mutane su yi shiru da bakinsu.

“Na fito na yi magana ne, saboda ba zan iya zura ido ina kallo mutane suna wasa da sunana ba. Dukkan abin da ake ta fada zance ne kawai.”

Gabanin kalaman na Ronaldo, kocin kungiyar ta Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce babu kamshin gaskiya a labarin

Yanzu haka ya ragewa Ronaldo shekara daya ne kwantiraginsa ya kare a kungiyar ta Juventus.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG