Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ronaldo Ya Zira Kwallo Ta 750


Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo.

Cristiano Ronaldo wanda dan asalin kasar Portugal ne ya zira kwallonsa ta 750 cikin shekarun da ya kwashe yana buga tamaula.

Ya samu nasarar yin hakan ne a lokacin da kungiyarsa ta Juventus ta doke Dynamo Kiev a gasar cin kofin zakarun turai.

Ya dai zira kwallon ne cikin ruwan sanyi, wacce aka doko ta daga kuryar gefen ragar.

An tashi a wasan da ci 3-0.

‘Yan wasa uku ne dama suke gaban Ronaldo a jerin wadanda suka yi fice wajen yawan kwallaye a riga, akwai kuma yiwuwar ya wuce su kafin karshen wannan kakar wasa idan har tauraruwarsa ta ci gaba da haskakawa.

Yanzu haka Pele wanda ke da kwallaye 767 na gaban Ronaldo da kwallaye 17 yayin da Romario ke da kwallaye 772, wato yana gaban Ronaldo da kwallaye 22 kenan.

Josef Bican ne ke gaba da yawan kwallaye da ba a tabbatar ba, amma rahotanni sun yi kiyasin yana da kwallaye akalla 805.

Kudi Bai Kare Shi Daga COVID-19 Ba: Cristiano Ronaldo Ya Kamu Da Cutar Corona
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:41 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG