Accessibility links

Rundunar Sojin Nigeria na Son a Yiwa Mutane 500 Shari'ar Aikata Laifukan Ta'addanci


Sojan Nigeria zaune cikin mota lokacin aikin sintiri. Rundunar sojin Nigeria a Maiduguri ke binciken gida-gida domin gano makaman da 'yan tsagera suka boye.

Laraba ce rundunar sojin Nigeria tace tana son ganin an gurfanar da mutane sama da dari biyar da ake kyautata cewar masu tsatsauran kishin islama ne, cikinsu harda jami'an tsaro dake basu goyon bayan shirya kai hare-haren ta'addanci, a gaban shari'a.

Rundunar sojan Nigeria ta bada rahoton cewa mutanen da ake zargi da aikata laifin shirya ta'addancin yanzu haka suna tsare a sansanonin soja dake Arewa maso gabashin Nigeria, kuma yawansu ya haura dari biyar.Kama mutanen ya biyo bayan wani matakin inganta harkokin tsaron ne da sojin Nigeria suka dauka na kokarin kawo karshen tada fitinar da aka shafe sama da shekaru hudu ke nan da 'yan kungiyar Islama ta Boko Haram ke addabar jama'a.

Daga cikin mutanen da ake tuhuma harda wani likitan fida, ko ayyyukan kiwon lafiya, da jami'an tsaron da suka hada harda soja da 'yan sanda wadanda ke bada goyon bayan tada kayar bayan da 'yan kungiyar ta'addancin keyi.Jami'in dake magana da yawun rundunar tsaron Nigeria, Chris Olukolade anji yana cewa akwai wasu manyan mutane masu fada aji a cikin gungun wadanda ake tsare dasu. Wasu a cikinsu kwarraru ne dake bada horo kan ayyukan ta'addanci da samar da makamai masu nagaarta. Yace akwai kuma wadanda da bakinsu suka tabbatar da cewa sun sami horonsu ne a kasar Mali da wasu kasashen dake makwabtaka da Nigeria. Idan za'a tuna, tsagerun da ake kayuatat cewar 'yan kungiyar Boko haram ne, sun afkawa sansanonin mayakan saman Nigeria da wasu muhimman wuraren ayyukan soja, rike da makamai suka rika harbe-harbe a wasu sassan birnin maiduguri dake Arewamaso gabashin Nigeria a ran litinin, hakan ya kuma karfafa ayyukan tada zaune tsaye da janyo barazanar rashin zaman lafiya a tsakanin al'ummar Nigeria dake zaman taurarauwa kasa mai albarkatun mai a nahiyar Afirka.

Rundunar soja a Nigeria ta kafa wani kwamatin kwararrun da zai gudanar da bincike da zai tantance na kwarai daga cikin mutane 1,400 da ake tsare dasu tun farkon tankade da rairayar da jami'an tsaron suka fara a yankin na Arewa maso gabashin Nigeria. A ran laraba ce aka ji jami'an rundunar sojin Nigeria na cewa har yanzu dai ana ci gaba da gudanar da binciken tantancewa kan wasu laifuka 600 da ake zargin aikatawa, an kuma kokarta baiwa hukumomi shawarar sakin wasu daga cikin wadanda ke tsare. A yanzu haka kuma babban Lauyan Gwamnati-ko (Atoni-Janar) yana nazartar wasu daga cikin takardun dake kunshe da bayanin shwarar abubuwan da za'a yi wajen shirya kai sauran masu laifin gaban shari'a. Shawarar tura wadanda ake zargi da aikata laifi gaban shari'a tazo ne a dalilin yawan wayar tarhon da aka rika samu daga kasashen Turai cikin 'yan watannin nan dake yin kira ga Gwamnatin Nigeria da ta yiwa Allah tayi amfani da doka da oda domin kare mutumcin Bil Adama a lokacin da take daukan matakan yaki da 'yan ta'addar Boko Haram da mukarrabansu.

Kungiyoyin kare hakkin Bil Adama, na zargin jami'an tsaro da daukan matakin neman shige gona da iri wajen azabtar da wadanda ake tuhuma, harma anyi zargin kashe wasu.Amma Gwamnati da rundunar sojan Nigeria duk sun karyata wadannan zargi. In an tuna, a watan Mayu ne shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta baci a jihohi uku dake Arewa maso gabashin Nigeria, sannan ya bada umarnin karfafa daukan matakan soja domin murkushe yunkurin tada kayar bayan da 'yan kishin Islama keyi. Dbun Dubatar mutanen ne suka halaka a wannan shekarar kadai a dalilin tashe-tashenu hankulan dake da nasaba da rikicin 'yan Boko Haram, kungiyar da burinta shine a kafa Gwamnatin Islama da a kuma yi aiki da dokar Musulunci a Nigeriar dake da jama'ar da yawansu ya kusa kaiwa miliyan 170 da suka rarrabu zuwa addinan Islam da na Kirista.Bugu da kari kuma, ana yawaita zargin kungiyar Boko Haram da yawaita kaiwa jami'an tsaro hari, da yawan kaiwa farar hula hari, ciki harda zargin kisan kare dangin da ake zargin Boko haram da yiwa Daliban Kwalejoji da yawaita kaiwa mujami'un Kirista harin bom, suna masallati ba'a barsu a baya ba, ballantana kasuwanni. Hakan ne kuma ya janyo hankulan kasa da kasa a watan Augustan shekarar 2011 lokacin da aka kaiwa ginin ofisoshin MDD hari a birnin tarayya na Abuja. Mutane 24 ne suka rasa rayukansu. Kungiyar kare 'yancin Bil Adama ta kasa da kaa"Amnesty International" ta fidda wata sanarwa a watan Oktoba dake cewa kusan mutane 1,000 ne suka rasa rayukansu mafi yawansu kuma 'yan tsagerar Islama dake damfare a gidajen kurkukun Nigeria a watannin shidan farko na wnanan shekarar. Amma Gwamnatin Nigeria tayi watsi da zargin da ake mata, harma ta bugi kirjin cewa ai yanzu al'amura sun fara daidaituwa.
XS
SM
MD
LG