Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rufe Iyaka Ya karya Wasu 'Yan Kasuwar Najeriya - Dan Iyan Nassarawa


Aminu Dan Iyan Nassarawa
Aminu Dan Iyan Nassarawa

‘Yan kasuwa da masu fiton kayaki a Arewa maso yammacin Najeriya, na ci gaba da kokawa da shiga halin “ni ‘yasu”, sanadiyyar matakin gwamnatin tarayyar kasar, na ci gaba da garkame kan iyakokinta.

Gwamnatin tarayyar dai ta ce ta dauki matakin na rufe iyakokinta ne saboda inganta sha’anin tsaro da habaka tattalin arziki a cikin gidanta, ta hanyar hana shigowa da makamai da kuma wasu haramtattun kayaki daga kasashen waje.

To sai dai kuma ‘yan kasuwa da dama ne ke korafin karyewarsu baki daya sanadiyyar matakin na gwamnati, lamarin da kuma suka ce ya jefa al’ummar yankin baki daya a cikin ukuba.

Aminu Dan Iyan Nassarawa, shugaban kungiyar masu fiton kayakin na hukumar kwastam, mai kula da yankin na arewa maso yamma, ya ce akwai yarjejeniya ta kasa da kasa akwai yarjejeniyar zamantakewa da kuma ‘yan ci na dan Najeriya da dan adam da yake da cikakken ikon ya koma duk inda yake so.

Amma yanzu duk wadannan abubuwan yanzu an taka su ba zaka iya fita ba ko kai waye ba zaka iya shigowa ba ko kai waye, illar da aka yi wa 'yan kasuwa babba ita ce na rashin ba su wa’adi kafin daukan wannan mataki.

Dan Iyan Nasarawa ya kara da cewa shin gwamnati za ta biya su asarar da suka yi, saboda akwai hukuma da take karfafawa mutane su ringa fitar da kayansu kasashen waje wanda har kudi ake ba da wa da wani ihsani domin a dauki kayayyakin da su ke yi a Najeriya a fitar da su makwabta.

Saurari cikakkiyar hirar da, wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna, ya yi da Aminu Dan Iyan Nassarawa, shugaban kungiyar masu fiton kayayyaki na hukumar kwastam mai kula da yankin arewa maso yammacin Najeriya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG