Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Saman Nigeria Ta Fara Aikin Inganta Tsaro A Kudancin Nigeria.


Sojojin tsaro a Maiduguri, Nigeria, Disamba 2013. (Heather Murdock for VOA)

Domin samar da tsaro a Nigeria rundunar sojojin Saman kasar tafara wani aikin inganta matakan tsaro a kudu maso gabashin kasar, inda yanzu haka aka aika musu da wani jirgin jet domin wannan aiki.

Rundunar sojan sama na Nigeria tabi sahun sauran bangarorin sojojin kasar domin samar da tsaro a kudancin kasar musamman kudu maso gabas.

Sanarwan dake dauke da sa hannun kakakin sojan saman kasar Manjo Janar Adetokunbo Adesanya tace yanzu haka an kai wa jami’an da zasu yi aiki wannan yankin kayan aiki, wadanda suka hada da wani jirgi kirar Alfa jet, wanda akace an tura domin ya samar wa sojojin da zasu yi wannan aiki kariya ta musamman.

Wasu daga cikin wuraren da wannan aikin zai shafa sun hada da yankin kudu maso gabashin Nigeria, da kuma yankin Niger Delta.

Ga L amido Abubakar Sokoto da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG