Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Kawancen Tafkin Tchadi Ta Rugurguza Sansanin ISWAP


Rundunar kasashen yankin tafkin Chadi

Dakarun kawancen kasashen yankin Tafkin Tchadi sun rugurguza wani babban sansanin mayakan ISWAP dake Fedondiya a yankin Tunbun fulani a zirin tafkin na chadi.

Sojojin Kamaru suna rangadi a tafkin Chadi
Sojojin Kamaru suna rangadi a tafkin Chadi

Kakakin rundunar kanar Timothy Antiga ya shaidawa Muryar Amurka cewa, dakarun MNJTF runduna ta uku sun farma mayakan na yan ta'adda ne daga bangaren Najeriya da manyan bindigogi.

Rahotanni dai sun tabbatar da sojojin rundunonin biyu sun yi wa yan ta'adda barna sosai yayin wannan gumurzu.

Kanar Timothy Antiga yace koda yake kawo yanzu ba a tantance girman barnar da aka yiwa kungiyar ISWAP, to amma bayanan farko da aka tattaro ta hanyar na'urori ya nuna an yi wa masu ikirarin jihadin gagarumar barna.

Wani masanin tsaro a yankin tafkin chadin, Dr. Abubakar mohammed Sani yace muddin dakarun suka ci gaba da kai irin wannan hari na hadin gwiwa ta sama da kasa, to ba shakka za a kawo yan ta'addan.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:

Rundunar Kawancen Tafkin Tchadi Ta Rugurguza Sansanin ISWAP:2:00
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00


Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG