Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

RUNDUNAR KWASTAM TA KAMA BUHUNAN SHINKAFA SAMA DA DUBU BIYU


Hamid Ali Mai Ritaya Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya

Rundunar Kwastam ta Najeriya tareda taimakon rundunar soja ta kama buhunan shinkafa sama da dubu biyu da ake kokarin shigowa dasu Najeriya.

Hukumar ta kiyasta kudin shinkafar kan Naira milytan dari uku, wadda kudin harajinta zai tashi kan Naira milyan 57.

shugaban rundunar Kwastam na shiyar Seme Alhaji Muhammadu Ali ne ya shidawa wakilin mu cewar sai da suka nemi taimakon sojoji saboda yawan motoci da suka yi jigilar kayan da ake kokarin ketarowa dasu zuwa Najeriya da kuma cijewa da masu kayan suka nuna.

Shugaban na Kwastam yace hukumarsa tayi damarar sa kafar wando guda da yan fasa kwauri kuma zasu tabbatar da sun hana shigowa da haramtattun kaya a Najeriya musamman wanda zasu yi illa ga lafiyar al’umma.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG