Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Mayakan Nijar Ta Ce Askarawanta Sun Kakkashe 'Yan Ta'adda A Sassan Dake Fama Da Matsalolin Tsaro


Sojojin Nijar.

Rundunar mayakan Jamhuriyar Nijar ta sanar cewa dakarun tsaro sun hallaka gomman ‘yan ta’adda a tare da wargaza ma’ajiyar kayayyakin ‘yan ta’adda a yammacin kasar banda wasu nasarorin da tace an samu a sauran yankunan dake fama da matsalolin tsaro.

A bayanan da sashen kula da hulda da jama’a a rundunar mayakan kasa ya bayar cikin sanarwar mako makon da ake aike wa manema labarai don sanar da ‘yan kasa aiyukan da jami’an tsaro suka gudanar a fagen daga a tsawon makon 1 sun ce hadin guiwar jami’an tsaron Nijer da Burkina ya hallaka ‘yan ta’adda 22 lokacin da suka yi masu kwanton bauna a wani wurin dake yammacin Nijer koda yake jami’an tsaro 4 sun jikkata a yayin wannan fafatawa.

Wannan na faruwa ne jim kadan bayan da wata rundunar sojan Nijer ta Operation Niyya dake aikin sintiri a yankin yammacin kasa ta ragargaza wasu wurare 3 da ‘yan ta’adda ke ajiye mai tare da karkashe wasu mutane 5 da ke aikin fake wadanan kayayaki ba’idin Babura 17 da askarawa suka yi raga raga da su.

Sanarwar ta ci gaba da cewa jami’an tsaro na barikin sojan sashe na 8 dake Dirkou a arewacin kasa sun yi nasarar kama Babura 23 da motoci 5 a wannan mako sannan a karkarar Dan Mani dake tsakiyar kasa rundunar tsaro ta Farautar Bushiya ta ceto wasu yara 2 da aka sace da nufin neman a biya kudin fansa yayinda a Gundumar Guidan Roumji dake wannan yanki aka kama motoci 2 shake da man fetur da yawansa ya haura lita 6550 wadanda ake kyautata zaton na amfanin ‘yan ta’adda ne.

Har ila yau a cikin wannan mako sashe na 4 na rundunar hadin guiwar kasashen tafkin Chadi wato MNJTF dake aikin tsaro a gabascin Nijer ta yi nasarar kama dimbin bahuhuwan cimaka da kifi da magunguna a hannun abokan gaba bayan da aka bankado wasu wuraren da ‘yan ta’adda ke ajiyar kayansu.

Haka kuma sanarwar ta rundunar mayakan Nijer tace askarawanta sun yi nasarar dakile wata nakiyar da mayakan kungiyar IS suka dasa a kewayen garin Baroua dake jihar Diffa.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:53 0:00

XS
SM
MD
LG