Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar MNJTF Ta Kubutar Da Ma'aikacin Jinkai Daga ISWAP


Tambarin Rundunar Dakarun Hadin Gwiwa ta MNJTF

Rundunar dakarun kawance na kasashen tafkin Chadi, (MNJTF a takaice) ta kubutar da wani ma’aikacin jinkai da ya kwashe watanni takwas a hannun kungiyar ISWAP wadda ta yi garkuwa da shi.

Ma'aikacin jinkan da ke aiki da wata kungiyar agaji ta kasa da kasa, tun a farkon wannan shekara ne kungiyar ISWAP ta sace shi daga yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin MNJTF Kanar mohammed Dole, ya ce ma'aikacin jinkan da ISWAP ta ke garkuwa da shi a tungarta dake zirin Tafkin Chadi, an kubutar da shi ne bayan wani mummunan farmaki da dakarun su suka kai da jiragen yaki, hade da ruwan boma bomai da rokoki a tungar yan ta'addan.

Hakan ya sa yan ta'addar suka tarwatse ta yadda mutanen ake garkuwa da su kowa ya kama gabansa. A wannan yanayi ne ma'aikacin jinkan ya tsere zuwa kasar Nijar, inda dakarun MNJTF suka karbeshi.

Bayan da aka duba lafiyarsa, hedikwatar sojojin kawancen ta tura jirginta mai saukar ungulu, inda aka dauke shi aka mayar da shi gida Najeriya.

Kungiyogin agaji dai sun nuna jin dadinsu bisa wannan ci gaba da aka samu. Dakta Sake Abba, na kungiyar agaji ta Smile Medical Mission dake aiki a shiyyar ya ce wannan labari mai karfafa gwiwa.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00


Facebook Forum

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG