Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar MNJTF Ta Sadaukar Da Watan Maris Don Kawar Da Boko Haram A Yankin Tafkin Chadi


Tambarin Rundunar Dakarun Hadin Gwiwa ta MNJTF
Tambarin Rundunar Dakarun Hadin Gwiwa ta MNJTF

Rundunar da ke yaki da mayakan Boko Haram a kan iyakar Najeriya da Kamaru, ta ce akalla mutane 3,000 ne suka rasa matsugunansu a wani sabon fada.

Masu kula da yan gudun hijira a sansanin Minawao da ke kan iyakar Kamaru da Najeriya, sun ce adadin mutanen da ke neman agaji a sansanin na karuwa a kowace rana.

Isaac Luka, shugaban masu kula da ‘yan gudun hijira na Najeriya a Minawao, ya ce fadace-fadacen da ake yi da fama da yunwa a halin yanzu na haifar da wani yanayin rayuwa da tuni ya yi muni a sansanin.

Ya ce “A kwai ‘yan Najeriya da suka fito daga al’ummomin da ke kusa da kan iyaka, an ba su wasu gonaki don su fara noman abinci, amma kakar bana ba ta yi kyau ba, kuma hare-haren da ake kaiwa kan iyaka ya sun tsere zuwa sansanin, sun kuma taimaka wajen raba dan abin da suke da shi, wasu suna sayar da itace don samun abin da za su ciyar da ‘ya ‘yansu."

Rundunar Tafkin Chadi MNJTF Ta Ceto Wasu Mata 43 Da Yara 30 Da Suka Tsere Wa ‘Yan Boko Haram/ISWAP
Rundunar Tafkin Chadi MNJTF Ta Ceto Wasu Mata 43 Da Yara 30 Da Suka Tsere Wa ‘Yan Boko Haram/ISWAP

A watan Yunin 2014 ne Luka ya tsere daga jihar Bornon Najeriya bayan da 'yan ta'addar Boko Haram suka kashe sama da mutane 20 a kauyensu ciki har da iyalansa.

Ya ce al’ummomin da ke kusa da sansanin su ma sun cika makil da yan gudun hijirar da ke tserewa yunwa da fada tsakanin sojojin gwamnatin Kamaru da mayakan Boko Haram a kan iyakar arewa da Chadi da Najeriya.

Toudje Voumou shine babban jami'in gwamnati a gundumar Mayo-Moskota.

Ya ce rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa dake kula da yankin tafkin Chadi, ko MNJTF ta kara yawan dakarunta a kan iyaka. Rundunar dai tana da dakaru daga Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

Voumou ya ce kusan makonni biyu ana gwabza kazamin fada tsakanin sojojin gwamnatin Kamaru da mayakan Boko Haram a bangarorin biyu na kan iyakar Kamaru da Najeriya. Kuma an kafa sansanonin soji da dama domin tunkarar mayakan Boko Haram da ke fakewa da muzgunawa fararen hula a kauyukan da ke kan iyaka.

Rundunar Haɗin Gwiwa Ta MNJTF Ta Ceto Mata 6, Ta Kashe ‘Yan Boko Haram 20
Rundunar Haɗin Gwiwa Ta MNJTF Ta Ceto Mata 6, Ta Kashe ‘Yan Boko Haram 20

Rudunar MNJTF ta sanar a watan Fabrairu cewa za a sadaukar da watan Maris, domin murkushe sauran mayakan Boko Haram a yankin kan iyaka.

Rundunar ta ce an kaddamar da hare-hare da dama kan maboyar Boko Haram, amma ba ta bayyana adadin mayakan da aka kashe ko kuma suka jikkata ba.

Ta kuma ce fadan na wannan watan ya raba akalla mutane dubu uku da muhallansu.

Gwamnatin Kamaru ta ce ya kamata farar hula su taimaka wa sojojin da ke yaki da ‘yan ta’addar ta hanyar kai rahoton duk wasu baki a kauyukansu. Gwamnati ta ce ta dawo da masu aikin sa kai da za su taimaka a yakin da ake yi da Boko Haram, ta hanyar kai rahoton wasu baki da mutanen dake dauke da makamai da ke boye a cikin daji ga sojojin gwamnati.

Olivier Guillaume Beer shine wakilin hukumar UNHCR a Kamaru. Da yake magana da gidan rediyon kasar Kamaru CRTV a wannan makon, ya ce yanayin jin kai ga mutanen da suka rasa matsugunansu abin damuwa ne matuka.

A wata ziyarar da ya kai kasar Kamaru a watan Afrilun 2022, babban jami'in kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya, Filippo Grandi, ya sha alwashin bayar da karin tallafi ga 'yan gudun hijirar da ke gujewa tashin hankali da bala'o'i.

Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta samu kashi 23 cikin 100 ne kawai na dala miliyan 100 da take bukata domin kula da karuwar bukatun 'yan gudun hijira a kasar.

A shekara ta 2009 ne dai hare-haren kungiyar Boko Haram ya barke a Najeriya, kafin ya bazu zuwa kasashe makwabta da suka hada da Kamaru da Chadi da Nijar.

Sama da mutane 36,000 ne aka kashe musamman a Najeriya, yayin da wasu miliyan 3 suka tsere daga gidajensu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Moki Edwin Kindzeka ne ya hado wannan rahotan daga birnin Yaounde na kasar Kamaru.

XS
SM
MD
LG