Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Amurka na Binciken Kashe Sojojinta Hudu a Nijer


Jim Mattis, Sakataren Tsaron Amurka

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis yace rundunar soja na binciken mutuwar sojojin Amurka hudu a Nijer da suka mutu a farkon wannan wata a hannun mayakar jihadin Islama.

Yayin da ake dawowa da gawar daya daga cikin sojojin a jiharsa ta Florida a wannan mako, Mattis yace rundunar zata fidda sabuwar sanarwa da zarar ta samu bayanai a cikin lokaci.

Yace ana bincike a kan rashi da muka yina dakarunmu. Mu a ma’aikatar tsaron muna son mu san abin da muke fadi kafin mu bayyanar dasu, kuma a wannan lokaci bamu da cikkan bayanai a kan wannan batu. Zamu fitar da bayanai cikin gaggawa kamar yanda zasu shigo mana saboda muna alfahari da dakarunmu. Kamar yanda kuka sani, muna gudanar da bincike duk lokacin da aka kashe mana sojoji.

An kashe sojojin ne a farkon wannan wata a wani kwantan bauna da mayakan jihadin Isama suka yiwa dakarun Amurka da na Nijer a wani fada da yyi sanadiyar kashe sojojin Nijer guda hudu.

Sanata John McCain mai yawan sukar lamirin shugaba Trump ya yi barazanar shigar neman izinin sammaci na Karin bayani a kan wannan hari.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG