Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Hallaka 'Yan Fashi 89 A Zamfara


Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce ta halaka wani gungun mayakan ISWAP a Kollaram dake zirin tafkin Chadi.

Hedikwatar tsaron Najeriya tac e ta tura jiragen yakin ta bayan tattara bayanan sirri akan wani sansanin mayakan Boko Haram a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta yi nasarar hallaka adadi mai yawa na ‘yan taddan.

Jami’n watsa labarai a hedikwatar sojojin Najeriya, Navy, Kwamanda Abdulsalam Sani ne ya bayyana haka, inda kuma ya ce, zasu ci gaba da yaki da ‘yan ta’addan.

Ya kara da cewa, sojojin da su ke karkashin rundunar “Operation Hadarin Daji” tare da hadin kan jami’an ‘yan sandan kasar, da sojojin kasar Jamhuriyar Niger, sun sami nasarar hallaka ‘yan fashi 89, kana ta kubutar da mutane 5, mata 3 da maza 2 da aka sace a garin gidan Jaja dake kan hanyar garin Zurmi, hedikwatar karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Ya ce, rudunar ta samu nasarar kwace makamai da dama da suka hada da bindigogi kira AK47, PKT da harsashai da alburusai. Sannan sun kubutar da Shanu 322, da babura guda 44.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG