Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kama Makaman Boko Haram


Sojojin Najeriya a tsaye kusa da wata mota mai dauke da bindiga da aka kwato daga hanun 'yan Boko Haram
Sojojin Najeriya a tsaye kusa da wata mota mai dauke da bindiga da aka kwato daga hanun 'yan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta kama "dumbin" makaman mayakan Boko Haram dake ta da kayar baya a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kwamandan runduna ta bakwai, Brig. Gen. Victor Ezugwu wanda ya tabbatar da lamarin ya yabawa dakarun na Najeriya da suka fito daga bataliya ta 21.

Wannan nasara da dakarun Najeriya suka samu, babban gibi ne ga mayakan na Boko Haram.

Hakan kuma na faruwa ne jim kadan bayan da sojojin Najeriyar suka dakile wani hari yayin da mayakan na Boko Haram suka yi yunkurin kutsa kai a cikin dajin Sambisa da safiyar yau Alhamis.

Dakarun sun yi nasarar dakile harin ne bayan arangamar da suka yi da mayakan na Boko Haram, inda rahotanni suka nuna cewa an kashe 15 daga cikin ‘yan Boko Haram kana aka jikkata wasu da dama.

Daga cikin makaman da aka kama akwai:

- Nau’oin bindigogi manya da kanana (12)

  • Nau’ukan bama-bamai
  • Jigidar harsashai kirar kungiyar tsaro ta NATO
  • Gurneti-gurneti 36

Rikicin Boko Haram, wanda ya faro tun daga shekarar 2009, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane kana ya tilastawa miliyoyin mutane ficewa daga gidajensu a Najeriya da sauran kasashe dake yankin Tafkin Chadi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG