Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Musanta Cewa Za Ta Fito Domin Hana Mutane Yawo


Wasu Sojojin Najeriya

Hedikwatar rundunar sojin Najeriya ta musanta zarge-zargen da ake ta yada wa masu cewa za a yi amfani da karfin soji domin tilasta wa mutane su zauna gida domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Hedikwatar ta ce wannan zancen bashi da tushe kuma ana yada shi ne domin saka wa ‘yan Najeriya tsoro a zukatansu.

Sanarwar da kakakin sojojin na najeriya kanar Sagir Musa ya sanya wa hannu, ya ce akwai bayanin da rundunar sojin ta yi ga jami’an ta inda aka umarci sojojin da su zauna cikin shirin ko ta kwana.

A cewarsa sai aka sauya ainihin labarin domin biyan wasu bukatu mara sa kyau.

Ya zuwa yanzu dai mutum 65 ne ke dauke da wannan cutar ta Coronavirus a Najeriyar.

Saurari wannan rahoton a sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:42 0:00


Facebook Forum

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni – Dan Kasuwar Gwari A Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG