Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Musanta Zargin Kashe Mutanen IPOB


Nnamdi Kanu, madugun masu fafutikar neman kafa kasar Biafra
Nnamdi Kanu, madugun masu fafutikar neman kafa kasar Biafra

Rundunar sojojin Najeriya ta musanta zargin kashe wasu magoya bayan kafa kasar Biafra ko IPOB a kauyen shugaban kungiyar Nnamdi Kanu

Rundunar sojojin Najeriya ta musanta wasu rahotannin dake nuna cewa dakarunta sun kashe mutane da dama a kauyen shugaban kungiyar IPOB dake fafutikar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.

Rundunar ta fitar da sanarwa cewa hotunan da kungiyar ta IPOB ke yadawa ta kafofin sadarwa domin nuna irin kisan gillar da sojoji suka yi masu na bogi ne.

AIG Hosea Hassan Karma mataimakin babban Sifeto Janar na 'yansandan Najeriya dake Umuahia yayi karin haske. Yana mai cewa yayinda sojoji ke sintiri kan titin da ya wuce gaban gidan Nnamdi Kanu yaran dake harabar gidan su ne suka dinga jifar sojojin da duwatsu da kwalabe. Su ma sojojin sai suka fara harbi sama domin su tsorata masu jifansu.

Bayan da sojojin suka wuce wata mata da ta isa wurin yaran sun sassareta da adda. Wani dansandan kwantar da tarzoma da yaje sayan katin tarho, shi ma sun kamashi sun sassareshi.

Wani dan kungiyar IPOB ya ce an kashe masu mutane kumanin 20 zuwa 30 kuma wasu da dama sun jikata tare da yin hasarar dukiyoyi. Ya sha alwashin zasu dauku matakin gabatar da maganar gaban kotun duniya da kungiyoyin kare hakkin bil Adama na kasa da kasa dominlalubo mafita.

Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG