Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojojin Ruwan Najeriya Ta Soma Sintiri Na Ukku Kan Tekun Kasar


Sojoji mayakan ruwa na Najeriya

Can baya rundunar ta kaddamar da irin wannan sintirin har sau biyu domin dakile aika aikar barayin teku dake fashi da makami sun sace jiragen ruwa da kayansu

Kwamanda Christian Ezekobe kakakin sojojin ruwan Najeriya yace daga watan Janairu zuwa na Afirilun wannan shekarar an samu aika aikar masu fashi da makami a kan teku har sau ashirin da biyar da kuma ta'adancin 'yan yankin Niger Delta.

Sintirin da suka yi ya taimaka wajen dakile ayyukan miyagun mutane akan teku da kuma kare kamfanonin man fetur dake yankin. Babban hafsan sojojin ne ya kirkiro da shirin sintirin domin a tabbatar da lafiyar mutane da dukiyoyi ta kawar da bata gari dake kan teku.

Barayin teku da sojojin ruwan Najeriya suka cafke
Barayin teku da sojojin ruwan Najeriya suka cafke

Shirin sintirin na farko ya kare ne a watan Yuni. Kana aka yi na biyu da ya dauki kwanaki sittin ana gwagwatawa da bata gari. Yanzu da shiri na biyu ya kare sai kuma na ukku.

Kwamanda Ezekobe yace tunda aka kaddamar da kashi na biyu ba'a samu fashi da makami a kan teku ba koda ma sau daya. Yace da yaddar Allah zasu yi kokari su cigaba da dakile aikace aikacen 'yan tsagera.

Wasu gungun barayin teku da suka shiga hannu
Wasu gungun barayin teku da suka shiga hannu

Wani Abubakar Abdulsalam kwararre a sha'anin ruwa yayi tsokaci akan wannan shirin na ukku. Yace sintirin ba zai samu nasara ba sai an samu hadin kan wasu kasashe da suke cikin kungiyar tsare tekun. Yace misali idan 'yan tsagera sun yi barna a yankin Najeriya da zara sun tsere zuwa yankin wata kasar a kan teku to ba za'a iya kamasu ba sai da hadin kai da yaddar mahukuntar kasar. Akwai iyakokin kasashe aka kowane teku.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

XS
SM
MD
LG