Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsagerun Niger Delta Avengers Sun Kai Hari Kamfanin Mai Na Chevron


Avengers
Avengers

Kungiyar Avengers ta ‘yan Niger Delta ta kaddamar da wani sabon hari kan kamfanin Mai na Chevron mallakar kasar Amurka.

Harin ya faru ne a shiyyar jihar Delta, kungiyar Avengers dai tace wannan hari alamu ne na jan kunne ga kamfanonin Mai dake yankin, domin tabbatar da cewa kungiyar zata aikata abin da ta furta yi. Haka kuma kungiyar ta ja kunnen sauran kamfanonin Mai da cewa su guji komawa bakin aiki har sai an kammala tattaunawa da ‘yan Niger Delta.

Sai dai kuma rundunar tsaro ta kasa ta tabbatar da cewa a tsaye take domin tabbatar da tsaro a yankin Niger Delta. Wakilin Muryar Amurka Sunusi Adamu ya zanta da mai magana da yawun hedikwatar tsaro ta kasa Birgediya Janal Rabe Abubakar, wanda yace sojojin Najeriya na nan domin ganin an sami tsaro da kwanciyar hankali a wannan yanki da kuma ko ina a fadin kasa.

Kungiyar Avengers dai tayi kaurin suna wajen kai hare hare a yankin Niger Delta, musamman kan kamfanonin Mai wanda har tayi sanadiyar koma bayan hakkar danyen Mai a Najeriya da kaso sama da Hamshin cikin Dari.

Dakarun tsaron gamayya a yankin Niger Delta sun baiyana cewa sun sami nasarar kama mutane Biyar da ake zargin masu fasa bututu Mai ne a yankin. Haka kuma an kwato wasu jiragen kwale kwale masu inji ga wadanda aka kama, runudnar dai tace ta hallaka wasu masu fasa bututun Mai su Bakwai a wata musayar wuta da akayi.

Yanzu dai batun tattaunawar da akeyi tsakanin kabilun yankin Nige Delta da wakilan ‘yan bindigar, da alamu dai yana cikin wani hali na rashin gaba, domin ana cikin tattaunawar sai kwatsam wasu ‘yan bindigar su kai hari.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

XS
SM
MD
LG