Rundunar ‘yan sandan Nigeria ta kaddamar da shirin wayar da kan jamaar kasa cewa beli kyauta ne.
Da yake kaddamar da shirin a Minna fadar gwamnatin jihar Niger, babban sufeto- janar na ‘yan sandan Nigeria, Ibrahim Idris yace zasu zagaye Nigeria kaf domin yin wannan yekuwar.
Yace mutane su kwana da sanin cewa beli a caji ofis kyauta ne, ba’a biyan ko sisi kwabo, don haka duk wanda ya bayar da wasu kudade da kuma wanda ya karba duk masu laifi ne.
Ga Mustafa Nasir Batsari da karin bayani.
Facebook Forum