Yanzu haka daya daga cikin ‘yan uwan wadanda aka sace yayi nasarar karbo mutane 3 daga cikin wadanda aka sacen.
Da yake yiwa wakilin sashen Hausa Isah Lawal Ikara karin haske game da karbo mutane 3 daga cikin wadanda aka sacen, daya daga cikin ‘yan uwan wadanda aka sacen Komrade Danjuma Sarki, yace mutanen dake satar nan fa suna da manya-manyan makamai.
‘’Da muka shiga wajen karbo mutanen nan su da bakin su sun gaya mun cewa kar muyi wani wahala, mu gaya wa ‘yan sanda ko gaya wa wani kafin inzo domin ko za a gaya musu, sun ma fada mani cewar wannan ranar larabar an basu labarin su auna, wasu mutane da zasu wuce wannan hanyar, shi yasa suka fito suka tsare wannan hanyar da wuri-wuri suka jima basu gansu ba ALLAH ya cece wadannan mutanen’’
To sai dai da wakilin Sashen Hausa Isah Lawal Ikara ya tambayi Komrade Danjuma ko yaya suka hadu da wadannan mutanen, nan ko ga abinda yake cewa.
‘’Sun kira ni muna ta tattaunawa har muka samu fahintar juna, muka yi ciniki, suka fada mani inda zan same su, sai da nayi sa’oi biyu ina jira, suka kira ni suka ce in shiga daji, na shiga daji suka sa na fara tafiya inyi nan, inyi nan, inyi can in tsallake wannan rafin su dawo dani nan, haka na dinga yi, a cikin dare ni kadai, tun daga karfe 7 har wurin goma saura, dajin kusa da rijana ne.
To da aka tambaye shi ko nawa ya biya sai yace wannan ba abu ne da za a bayyana ba, amma dai mun bada wani abu.
Yace mutane 3 aka sako masa amma kuma yaje ne da niyyar mutun daya ne.Yace wadannan mutanen sunfi su 40 a cikin dajin nan, da makamai na zamani masu kyau, wannan yasa ake samun matsalar tsaro a jihar Kaduna
Facebook Forum