Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yansandan Borno Ta Tabbatar da Mutuwar Mutane 14 Sanadiyar Harin Boko Haram


IBRAHIM K. IDRIS, babban sifeton rundunar 'yansandan Najeriya
IBRAHIM K. IDRIS, babban sifeton rundunar 'yansandan Najeriya

Jiya Laraba ne da wajejen karfe bakwai na yamma wasu 'yan Boko Haram suka yi kokarin kutsawa cikin birnin Maiduguri inda suka tada bamabamai a wasu wurare da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 14 tare da jikata wasu da dama.

Yanzu yau rundunar 'yansandan jihar Borno ta tabbatar da mutuwar mutane 14 tare da wasu 24 da suka jikata sakamakon kunar bakin waken da wasu 'yan kungiyar Boko Haram suka kai.

A daidai lokacin ne kuma wasu 'yan Boko Haram suka yi kokarin kai hari a Jiddar-Polo wata unguwa a birnin Maiduguri.

Kwamishanan 'yansandan jihar Mr. Daniel Chukwu ya shaidawa manema labarai cewa bam din farko ya tashe ne a kauyen Kacallari dake karamar hukumar Jeni yayinda mutane ke fitowa daga sallar magariba inda mutane shida suka mutu da kuma wasu 24 da suka samu raunuka daban daban..

Akwai kuma wani bam din na biyu da ya tashi a wuraren yankin Chad Basin wanda ya kashe mutane uku. A nan bangaren kuma bam na uku ya tashi da ya kashe mutum guda.

Kokarin da 'yan Boko Haram suka yi na kutsawa cikin birnin Maiduguri ta Jiddari-Polo ya haddasa mutuwar mutum daya wanda har yanzu ba'a tantanceshi ba.

Tun a daren jiya din ne sojoji da 'yansanda suka dakile harin, inji kwamishan 'yansandan, lamarin da ya sa wadanda suka arce daga gidajensu sun soma komawa.

Kawo yanzu an kame wani dan Boko Haram daya kana an kashe wasu guda uku sakamakon musayar wuta da suka dinga yi da jami'an tsaro.An kuma gano wasu bindigogi kiran AK47 da wasu bamabamai kiran gida.

Maharan Boko Haram din sun kone gidajen 'yan gudun hijira guda ishirin wadanda suke daf da shiga cikin garin Maiduguri.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG