Accessibility links

Rundunar 'Yansandan Jihar Neja Ta Yi Shirin Tabbatar Da Tsaro


Rundunar 'Yansandan Najeriya

Wasu bata gari sukan labe da bukuwa kamar na kirsimati su aikata ta'asa dalili ke nan da rundunar 'yansandan jihar Neja ta yi shirin tabbatar da tsaro lokacin bikin kirsimati da sabuwar shekara.

Rundunar 'yansandan jihar Neja ta ce ta yi shiri na musamman domin tabbatar da an yi bukukuwan kirsimati da na sabuwar shekara lafiya a duk fadin jihar.

Kwamisahaniyar jihar Desire Nzirim ta ce kowane lokaci suna iyakacin kokarinsu na tabbatar da lafiyar al'umma to amma wannan lokaci lamarin na musammana ne. Yakin Suleja na cikin wuraren da 'yansanda suka fi mayarda hankali ganin irin abubuwan da suka faru a baya na tashe-tashen bamabamai da suka hada da na mijami'ar St Theresa na garin Madalla da aka kai ma hari a ranar kirsimatin 2011.

Kan garin Suleija da kewaye kwamishaniyar ta ce sun yi irin nasu binciken, sun tanadi kwararun jami'ai da wadanda suka kware kan bama-bamai domin dakile duk abun da ka iya tasowa. Ban da haka sun yi shirin ko ta kwana. Ta ce da hadin kan jama'a za'a yi bukukuwa cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Ita ma gwamnatin jihar Neja ta ce tana iyakacin kokakrinta na tabbatar da cewa an yi bukukuwan lami lafiya. Alhaji Sule Haruna kwamishanan addinai na jihar ya ce suna kokarin su tabbatar an yi bikin lafiya. Ban da haka gwamnati tana rabawa kiristoci a duk kananan hukumomi kayan masarufi.

Ita ma kungiyar kiristoci ta jihar Neja wato CAN ta ce ta gamsu da matakan da aka dauka dangane da lamarin tsaro lokacin bukukuwan kirsimati. Shugaban CAN na jihar ya ce sun ji dadi. Dangane da hukuncin daurin rai da rai da aka yiwa Kabiru Sokoto wanda ya shirya harin da aka kai kan mijami'ar Madalla shugaban CAN Rebaran Musa Dada ya ce sun gamsu da hukuncin.

Mustapha Nasiru Batsari nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG