Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yansandar Jihar Taraba Ta Kama Barayin Shanu


Barayin shanu

Kwamishanan 'yansandan jihar Taraba Mr. Yakubu Yonana Babar ya bayyana kama wasu barayin shanu dake kokarin tserewa da shanun da suka sace

Shanun da suka sata sun kai kimanin dari da arba'in da biyu da kuma tumaki ishirin da shida duk daga yankin Gashaka dake tsakiyar jihar.

Kwamishanan yace an ga mutanen da shanu da tumakai ne da ake kyautata zaton na sata ne. Da suka samu labarin ne ya sa suka tura jami'ansu wadanda suka kama mutanen.

Wai da mutanen suka ga jami'an tsaro sai suka bude masu wuta da bindigogi. Amma jami'an tsaro sun samu nasara a kansu.

Yan Bindiga Barayin Shanu
Yan Bindiga Barayin Shanu

Baicin barayin shanu, rundunar 'yansandan ta samu cafke 'yan fashi da makami da kuma masu garkuwa da mutane domin samun kudin fansa wadanda suka matsawa wasu kananan hukumomi.

Rundunar 'yansanda ta kuma cafke wani da ake zarginsa da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba. An sami mutumin da bindiga kirar AK 47 da harsashai ishirin da shida.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG