Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Na Kokarin Kaiga Kungiyar Boko Haram


Shugaba Buhari da Buratai

Gwamnatin Najeriya ta ce ta na kokarin kaiwa ga kungiyar Boko Haram, bayan da wani faifain bidiyo ya fito jiya Lahadi, wanda ke nuna kusan ‘yan matan Chibok 50 daga cikin sama da mata 200 da aka sace a shekarar 2014.

Kungiyar dai ta ce da yawa daga cikin ‘yan matan sun mutu, kuma suna bukatar a yi musayar fursunoni da gwamnatin ta Najeriya.

Faifan bidiyo mai tsawon minti 11, wanda aka wallafa shi a kafar sadarwa ta Youtube, ya nuna wani mutum lullube da fuska sanye kuma da kakin sojoji, yayin da wasu ‘yan mata da dama ke zaune, wasu kuma ke tsaye a bayansa sanye da hijabai.

Cikin harshen Hausa, mutumin ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta saki ‘yan uwansu da ake tsare da su a Abuja da Legas da kuma Maiduguri.

Wannan dai ba shi ne karon farko da kungiyar ta Boko Haram ta mika irin wannan bukata ba, kuma masu fafutukar ganin an sako ‘yan matan sun ce, ko dan saboda wadannan dalibai, lokaci ya yi da hukumomin Najeriya za su bude kofar tattaunawa da mayakan na Boko Haram.

XS
SM
MD
LG