Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yansandan Kano Ta Kama Matasan dake Sace Mutane


Wasu cikin matasa masu sace mutane da 'yansandan Kano suka cafke a dajin Falgore

Bayan ta fafata dasu a dajin Falgore, rundunar 'yansandan Kano ta cafke wasu matasa da suke sace mutane tare da kubutar da wasu da suke tsare dasu cikin dajin.

Cikin wadanda aka kubutar har da wata da tace miyagun mutanen sun je gidansu ne da tsakar dare suka yi awan gaba da ita da tare da fada mata su tanadi kudi kamar rabin miliyan na nera cikin kwanaki ukku ko kuma su kasheta.

Shi kuma wani da ya fada hannunsu yace sun daukeshi tare da kakarsa bayan sun yi harbin da ya kashe kanin mahaifinsa. Barayin sun daddauresu kana washegari suka dinga zuba masu bulala. Bayan dukan sun kira mahaifinsu wai ya basu nera miliyan biyar da rabi. Wannan dan taliki yayi kwana goma sha daya a hannun mutanen.

Masu sace mutane da 'yansandan Kano suka cafke a dajin Falgore
Masu sace mutane da 'yansandan Kano suka cafke a dajin Falgore

Rundunar 'yansandan ta Kano ta samu nasarar kama matasa goma sha biyu daga cikin matasan da ake zargi suna boye mutanen da aka sace a sansanoninsu dake cikin dajin Falgore.

Kwamishanan 'yansandan Kano yace matasan sun fito ne daga jihohin Kano da Kaduna da kuma Bauchi an kamasu da bindigogi da albarusai dari biyu da hamsin da kayan maye na hodar iblis da kudi da baburan hawa da kayan dafa abinci da wayar hannu.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

XS
SM
MD
LG