Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rusa Ofishinmu A Gombe Kokarin Ta Da Husuma Ne – PDP


Taron majalisar zartarwar jami'iyyar PDP a Najeriya (Hoto: PDP)
Taron majalisar zartarwar jami'iyyar PDP a Najeriya (Hoto: PDP)

"Jam’iyyar PDP na kira ga gwamnatin jihar Gombe da ta yi maza-maza ta sake gina mana ofishin kamfen dinmu tare da neman afuwar al’umar jihar." PDP ta ce.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta yi tir da rusa ofishinta da aka yi a jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook dauke da sa hannun Sakataren yada labaranta, Debo Ologunagba, PDP ta kwatanta rusa ofishin nata a matsayin tsokana, tana mai cewa hakan, alama ce gwamnatin APC da ke mulkin jihar na fargabar cewa PDP za ta kwace mulki a 2023.

“Gwamna Inuwa Yahaya ya tsorata da ofishin kamfen din PDP a jihar ta Gombe, wanda ya zama mahadar jama’a a wani yunkuri na kwato jihar daga gwamnatin APC.

“Saboda haka, jam’iyyar PDP na kira ga gwamnatin jihar Gombe da ta yi maza-maza ta sake gina mana ofishin kamfen dinmu tare da neman afuwa daga al’umar jihar. Sanarwar ta Ologunagbo ta ce.

Jam'iyyar APC ce ke mulki a jihar ta Gombe karkashin Gwamna Inuwa Yahaya.

Yayin wata ganawa da manema labarai da ya yi, shugaban hukumar kula da tsarin birnin Gombe Peter Bilal, ya ce rushe-rushe da suke yi, ba su da nasaba da siyasa, illa kokari ne ake yi na tabbatar da an bi tsarin jadawalin birnin kamar yadda aka tsara tun a 2001, a cewar jaridar Vanguard.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG