Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Ba Za Ta Kai Labari Ba A Zaben 2023 – PDP


Lokacin da aka zabi Ifeanyi Okowa, hagu, a matsayin abokin takarar Atiku, dama (Hoto: Facebook/PDP)
Lokacin da aka zabi Ifeanyi Okowa, hagu, a matsayin abokin takarar Atiku, dama (Hoto: Facebook/PDP)

Ita dai jam'iyyar APC mai mulki ta ce lokaci kawai take jira ta lashe zaben wanda za a yi a watan Fabrairun badi.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta yi kira ga jam’iyya mai mulki ta APC, da kada ta bata lokacin wajen yin yakin neman zabe, domin ba inda za ta je a zaben 2023 da ke tafe.

PDP ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun sakataren yada labaranta na kasa Hon. Debo Ologunagbo, tana mai cewa, jam’iyyar ta APC ba za ta iya samun ko da kashi 25 cikin 100 a dukkan jihohin kasar ba.

“Dandazon mutanen da suka halarci gangamin da PDP ta yi a jihohin Kano da Katsina, alamu ne da ke nuna cewa mutane sun yi watsi da APC.” Sanarwar ta ce.

Lokacin da shugaba Buhari ya ba Tinubu tutar jam'iyya (Hoto: Fadar shugaban kasa)
Lokacin da shugaba Buhari ya ba Tinubu tutar jam'iyya (Hoto: Fadar shugaban kasa)

“Karbe ofishin kamfen din shugaban kasa da PDP ta yi a jiharsa ta Katsina, bayan da wasu kusoshin APC suka fice daga jam’iyyar, wata alama ce da ke nuna cewa, mutane sun dawo daga rakiyar jam’iyyar.”

“Idan za a yi zabe na hakika, wanda babu magudi, APC ba za ta taba samun kashi 25 na kuri’u ba, a mafi aksarin jihohin kasar.” PDP ta ce.

Jam’iyyar APC a baya-bayan ta yi nuni da cewa babu haufi ita za ta lashe zaben na 2023.

“Muna kirga kwanakin da suka rage mana da za mu samu nasara da izinin Allah.” APC ta ce a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Facebook, tana mai cewa lokaci kawai take jira ta lashe zaben.

XS
SM
MD
LG