Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwa da Tabo Ya Shafe Garin Macoa


Ambaliyar Koguna har guda uku sakamakon ruwan sama mai tsananin yawa ta sa ruwa da tabo ya shafe garin Macoa dake kudu maso yammacin kasar Colombia a daren Juma’a yayin da mazauna a yankin ke bacci, Ambaliyar ta rushe gidaje da gine gine wanda yayi sanadiyar mutuwar kimanin mutane 200.

Shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos ya ziyarci garin mai yawan alumma 40,000 wanda ke kusa da iyakar Colombia da Ecuador a jiya Asabar inda ya ayyana rana ce ta tashin hankali.

Santos yayi gargadin yiwuwar karuwar yawan wadanda suka rasu inda yace “Bamu san adadin wadanda abin yashafa ba.”

Ya kara da cewa, “wadanda wannan al’amari ya shafa zamu iya baki kokarin mu muga mun taimaka musu, wannan abu ya sosamin rai.”

Daga bangaren Kungiyar Agaji ta Redcross kuwa jami’ai sun bayyana cewar mutane 400 ne suka jikkata yayin da kimanin 220 suka riga mu gidan gaskiya wasu da yawa kuma ba’a gansu ba.

Masifar ta afku ne sakamakon kwanaki da aka kwashe ana zabga ruwan sama wanda ya jawo daukewar wutar lantarki da kuma ruwan famfo.

A ‘yan watannin nan ruwan sama mai yawa ya jawo ambaliyar ruwa a Yankin Amurka ta Kudu dake gefen Pacific wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a kasashen Peru da Ecuador.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG