Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwan Sama Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Akalla Mutane 40 A Kenya


Wasu da suka samu tsira daga ambaliyan ruwan da ya rabasu da muhallansu

Ruwan da aka yi kamar da bakin kwarya a Kenya ya hallaka akalla mutane 4o tare da raba wasu dubu 220 da muhallansu

A kalla mutane 40 ne suka mutu sakamakon rushewar madatsar ruwa a kasar Kenya ranar Laraba bayan anyi ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Wannan ruwan ya share gidaje da dama da gonaki tare da tsayar da harkokin kasuwanci bayan Dam din dake Solai kilomita 180 a arewa maso yammacin Nairobi yayi ambaliya.

Ian Ndegwa wanda yaga yadda lamarin ya faru ya fada wa sashen Swahili na Muryar Amurka cewa adadin rayukan da suka salwanta na iya zarta abinda aka bada rahoto akai.

Domin akwai mutane da dama da har yanzu ba’a san inda suke ba. Yace akwai ‘yan sanda da sojoji dama magina suna wannan wurin domin ganin sun kwashe abubuwan da suka toshe hanya tare da neman mutanen da suka bata.

Gwamnatin kasar Kenya ta fada a ranar Laraba cewa sakamakon wannan ruwan saman yayi dalilin raba mutane da yawan su ya kai dubu 220 da muhallan su.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG