Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Madatsar Ruwa A Wani Kwazazzabo Yayi Ambaliya A Kenya


Wata madatsar ruwa a wani kwazazzabo dake kasar Kenya ya goce a daren jiya, inda ya kashe mutane akala 27.

Ruwan da yayi ambaliya ya tafi da gidaje da wuraren sana'oi'in mutane bayan da ya kwararo daga madatsar ruwan din Patel a yankin Solai, kimaninKilo mita 150 daga arewa maso yammacin birnin Nairobi.

Jami'ai sun ce sun ceto kusan mutane 40 kuma an kai su asibiti, kuma ma'aikatan agaji na cigaba da neman mutanen da watakila suka makale suka kasa fitowa.

Wata biyu kenen yankin ke ta samun ruwan sama mai karfi, wanda ya ke ta hadasa ambaliyar ruwa da tabo tabo da yayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 130.

Gwamnatin Kenya jiya laraba ta ce ruwan saman yayi sanadaiyar batar da mutane dubu dari biyu da ashirin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG