Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwan Bamabamai Ya Kashe Wani Mai Aikin Bada Agaji a Kasar Ukraine


Alexander shugaban 'yan tawayen Ukraine

Yayin da dakarun gwamnati da na 'yan tawaye ke cigaba da fafatawa ruwan bamabamaisun rutsa da ofishin kungiyar bada agaji wanda yayi sanadiyar mutuwar daya daga cikinsu.

Ruwan bamabamai akan birnin Donetsk a gabashin Ukraine jiya Alhamis ya hallaka wani dan kasar Swizerland dake aiki da kungiyar agaji ta kasa da kasa wato Red Cross ko ICRC a takaice.

‘Yan jarida na kasashen yammacin turai dake cikin Danetsk da kafofin labaran kasar Rasha sun ruwaito cewa bam ya fada kan ginin ofishin ICRC dake tsakiyar yankin ‘yan tawaye. Kungiyar ICRC ta tabbatar da mutuwar daya daga cikinsu wanda tace dan kasar Swizerland ne.

Haka kuma jiya Alhamis an sanar da aukuwar mummunan gwabzawa kusa da filin saukar jiragen sama a Danetsk yayin da masu samun goyon bayan Rasha suka cigaba da kutsa kai domin su kwato wasu wurare daga hannun dakarun gwamnati.

Idan ba’a manta ranar 5 ga watan Satumba gwamnatin Ukraine da ‘yan tawaye masu samun goyon bayan Rasha suka raftaba hannu a kan wata yarjejeniya amma duk d ahaka sun cigaba da fada jefi jefi saidai lamarin ya fi Kamari wannan makon musamman a wajejen Danetsk. A kalla mutane 10 ne suka mutu sanadiyar bamabamai akan birnin.

A wata sabuwa kuma Shugaban Rasha Vladimir Putin ya fada jiya Alhamis cewa kasar Ukraine nada damar komawa kan hadin kan ‘yan kasar ta tabbatar da habaka tattalin arzikin kasar idan zata ba kowa kowa cikakken hakinsa.

Yayin da yake Magana a wani dandalin zaka jari a Moscow Mr. Putin yace duk wanda yake zaune a Ukraineya kamata yana da cikakken haki a karkashin dokokin kasa da kasa da na Ukraine. Kada a nuna wariya sabili da banbancin harshe, kabilanci ko addini.

Yace wannan ita ce kadai hanyar da kasar zata zama tsintsiya madaurinki daya.

Kamfanin labaran Reuter ya Ambato wani mai Magana da yawun NATO yana cewa daruruwan dakarun Rasha da suka hada sojoji na musamman suna cikin kasar Ukraine yayi da aka jibge sojoji Rasha kusa da 20,000 kusa da iyaka da gabashin Ukraine.

XS
SM
MD
LG