Iyalan tsohuwar ‘yar takarar shugaban kasar Rwanda na neman karin haske kan halin da take ciki, mako guda bayan da ‘yan sanda suka kama ta.
A hukumance, ita wannan maccen mai suna Diane Rwigara ana tuhumarta da laifukan da suka shafi tsaron kasa da kuma jabu, bayan da aka kamata ranar 23 ga watan Satumba. To amma iyalanta sunyi imanin laifinta kadai shine neman kalubalantar shugaba Paul Kagame, na tsayawa takarar shugaban kasa.
A cewar wani ‘dan uwanta, Rwigara Aristide Rwigara, wanda yake zaune a Amurka “Wannan tuhuma da ake mata karya ne, kuma babu wani a Rwanda da yayi imanin gaskiyar tuhumar da ake yi mata. Kowa yasan an kirkiresu ne kawai.”
Kungiyoyin kare hakkin ‘dan Adam, sun zargi jam’iyyar shugaban kasa Paul Kagame, da cin zarafin ‘yan adawa ta hanyar amfani da barazana wajen rufe bakinsu.
Tun shekarar alif 994 Kagame yake mulkar kasar Rwanda, kuma a watan Agustan wannan shekara ne aka sake zaben shi a wa’adi na uku na mulki.
Facebook Forum