Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutum dari biyu da tamanin da hudu da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar.
A sanarwar da ta fitar ta shafin twitter a daren ranar Laraba 20 ga watan Mayu, hukumar ta ce an samu sabbin kamu mutum dari ta cisi’in da tara a jihar Legas, ashirin da shida a jihar Rivers, sha tara a Oyo, takwas a babban birnin tarayya Abuja, takwas a Borno, bakwai a Filato, shida a Jigawa, biyar a Kano.
Sauran jihohin da aka samu karin mutum daya daya da suka kamu da cutar sun hada da Taraba, Delta, da Kwara a cewar sanarwar.
Ya zuwa yanzu dai gaba dayan adadin wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 a Najeriya ya kai 6677.
Sanarwar ta kuma ce an sallami mutum 1,840 daga asibiti, bayan haka mutum 200 suka mutu sakamakon cutar.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 20, 2023
Gwamnonin Gombe, Bauchi Sun Samu Wa'adi Na Biyu
-
Maris 19, 2023
Seyi Makinde Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Oyo
-
Maris 19, 2023
Yadda Aka Yi Zaben Gwamna A Bauchi
Facebook Forum