Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabbin Gwamnoni Sun Fara Ciwo Bashi


Gwamnan Jahar Borno Kashim Shettima da na Bauchi Muhammed Abdullahi Abubakar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan Benue Samuel Ortom, a wata ziyara da suka kaiwa mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo
Gwamnan Jahar Borno Kashim Shettima da na Bauchi Muhammed Abdullahi Abubakar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan Benue Samuel Ortom, a wata ziyara da suka kaiwa mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo

Wani kwararre a harkan tattalin arziki a Najeriya , Yushau Aliyu yayi gargadi.

‘’Bashi wanda aka ciwo kuma ba tabbatar da abinda akayi da bashin ba, kuma aka shiga matsala gwamnati bata iya biyan albashi, shine kaskantaccen yanayi da gwamnati zata samu kanta, akan ciwo basussuka ne domin ayi manyan ayyuka da suka zama wajibi ayi su, idan a yanayin da tattalin arziki ke tafiya, idan wannan jihar ta ciwo waccan ta ciwo haka ita gwamnatin tarayya taje ta ciwo bashin akan harkokin tsaro wannan yana da girma tunda kasafin kudin kasar wanda akayi wa gibi ne da yawa, duk gibin da suka shiga cikin kasafin kudi tunda a zahirin gaskiya duk kasafin kudin da aka yi ana yinsa ne a bisa kididdigar abinda gwamnati zata iya samu na kudaden shigan ta.Yin haka ana jefa tattalin arzikin jihohi cikin rudani, kuma gwamnonin ba zau fita cikin rudani ba, haka kuma ana kara jefa tattalin arzikin kasar cikin rudani sabo da irin abinda ya fara bayyana duk irin cin basussukan da ake yi a Najeriya wanda kanfanin J T Morgan shi ya fara sawa kasar takunkunmi aka cire ma daga jerin wadanda za a yi baiwa bashi sabo da ana duba yanayin halin da tattalin kasar yake.’’

Shima tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Abdul kadir Balarabe Musa masani harkokin tattalin kasa yace matsalar Najeriya ba wai rashin kudi bane wanda zaisa ta rika cin bashi. Ga dai abinda tsohon gwamnan ke cewa.

‘’Akwai kudin Najeriya bata cikin matsalar rashin kudi da zata rika cin bashi matsalan Najeriya shine banna, shine kawai matsalar Najeriya.’’

Ga Hassan Maina Kaina da Karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG