Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabbin Ministocin Najeriya Sun Fara Aiki


Sabbin ministocin Najeriya

Da alamar gwamnatin Najeriya za ta fara aiwatar da abubuwan da ta yi alkawarinsu ga 'yan kasar gadan-gadan daga yanzu ganin sabbin ministocinta sun tare a ofisoshinsu a Abuja, babban birnin kasar

Sabbin ministocin Najeriya 36 sun fara aiki gadan-gadan a ofisoshinsu da ke Abuja.Tuni masu tsokaci ke tofa albarkacin bakinsu kan dacewa ko rashin dacewar irin ma’aikatar da aka tura minister. Wani dan adawa mai suna Jauro Hammadu Sale ya ce Najreiya na da matukar arziki amma jama’a na cigaba da fama saboda an kasa zama a nemi mafita da gaske. Y ace sam ba daidai ba ne a rinka wahal da mutane don bukatar wani kawai.

To amma shi kuma wani tsohon Sanata mai suna Alkali Jajere y ace wasu ‘yan Najeriya sam bas u da hakuri, wanda ake matukar bukata ganin irin matsalolin da wannan gwamnatin ta tarar. Yan a mai kiran ‘yan Najeriya da su yi taka tsantsan kar Allah ya jarabce su saboda rashin godiya da wuyan sha’ani.

Shi kuwa wani jigon jam’iyyar APC mai mulki mai suna Muhammadu Inuwa Yahaya kira ya yi ga ‘yan Najeriya su yi aikinsu tsakani da Allah; ita ma gwamnati ta yi abin da ya wajaba akanta na kyautata ma jama’a da kasa.

Ga wakilinmu Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG