Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wanene Sabon Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya?


Antonio Guterres dan takarar zama babban sakataren MDD
Antonio Guterres dan takarar zama babban sakataren MDD

Rahotannin da bana hukama bane na nuna cewa an zabi tsohon Fara Ministan Portugal Antonio Guterres, ya zama sabon babban sakataren MDD.

Ana sa ran cewa nan bada dadewa ba za a tabbatar da shi a hukumance akan wannan mukamin.

Bayan an jefa kurji’un da kusan duk na bangare daya ne a jiya a zauren babban kwamitin zartaswa na MDD, aka fahimci cewa wannan tsohon dan siyasa kuma jami’in diplomasiyar ya yi galaba da kuru’u 13 da ya samu, kuma babu wanda ya nuna rashin amincewa koda yake akwai kasashe biyu da suka kaucewa jefa kuri’unsu.

XS
SM
MD
LG