Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Fada Ya Barke a Tripoli Bayan Da Dan Gaddafi Ya Karyata Nasarar 'Yan tawaye


Hayaki ke ta tashi a sashen Bab Aziziya da ke Tripoli
Hayaki ke ta tashi a sashen Bab Aziziya da ke Tripoli

Sabon fada ya barke a Tripoli, babban birnin kasar Libiya, ‘yan awoyi bayan da wani dan

Sabon fada ya barke a Tripoli, babban birnin kasar Libiya, ‘yan awoyi bayan da wani dan Gaddafi da ada ake ganin shi zai gaje shi, mai suna Seif al-Islam, ya bayya cikin birnin ya kuma ce gwamnatin ubansa na nan daram.

Mummunan fada ya barke a kusa da gidan Shugaba Gaddafi na Bab al-Aziziya a sa’ilinda barin wutar bindiga da bama-mai su ka yi ta girgiza birnin, wanda ‘yan tawayen ke ikirarin kusan ilahirinsa na karkashin ikonsu a yanzu.

Seif al-Islam ya bayyana kansa ga ‘yan jaridun kasashen wajen da ke otal din Rixon da ke sashen da ke karkashin ikon Gaddafi, duk ko da ikirarin shugabannin ‘yan tawayen cewa ya na hannun dakarunsu. Sannan sai ya zagaya da tawagarsa a sashen da har yanzu ke karkashin ikonsu, inda hotunan talabijin su ka nuna shi ya na ta daga hannu magoya baya kuma na ta yabawa.

Kotun aikata manyan laifuka ta karyata wani rahoton jiya Talata cewa ta tabbatar da damke Seif al-Islam, Kotun t ace bat a sami wani bayani ba a hukumance daga Majalisar Shugabancin Wucin Gidan Libiya ba.

Wata kafar shugabannin ‘yan tawayen t ace wani dan Gaddafin mai suna Mohammad, shi ma ya kubuce daga tsare shi da aka yi a gidansa ranar Litini. To amman da alamar dan Gaddafi na uku har yanzu yana kame, kuma ba a san inda Gaddafi yak e ba har yanzu.

Shugaban Majalisar Shugabanci ta ‘yan tawayen Mustafa Abdel Jalil, y ace za a yi adalci wajen shari’ar Gaddafi idan aka damke shi, kuma cikakkiyar nasara za ta tabbata ne lokacin da aka kama shi.

XS
SM
MD
LG