Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Jirgin Yakin Sojojin Ruwan Najeriya Yana Kan Hanya Daga China


Jirgin yakin sojojin ruwa.
Jirgin yakin sojojin ruwa.

Gwamnatin Najeriya na samarwa da rundunar sojojin ruwan kasar manyan jiragen yaki na zamani.

Yazu haka dai gwamnatin tarayya na ci gaba da mayar da hankali wajen samar da jiragen ruwan yaki ga rundunar ruwan sojojin Najeriya. A karo na biyu katafaren jirgin yakin da Najeriya ta sayo daga kasar China, ya isa kasar Angola kan hanyarsa ta zuwa Najeriya.

Daraktan watsa labarai a hedikwatar sojojin ruwan Najeriya, Komanda Christan Ezekobe, yace rundunar sojojin ruwan Najeriya suna ci gaba da samun manyan jiragen yaki irin na zamani da ake ji da su a wannan karni. Ya kuma ce jirgin farko ya isa Najeriya a bara, wannan kuma gashi yana kan hanya, wanda idan aka kaddamar da su zasu taka rawa sosai wajen samar da tsaro ta cikin ruwa.

Yanzu dai sojojin ruwan Najeriya zasu fara sintiri har zuwa gabar kotun Guinea. A cewar kwararre kan sha’anin tsaro Kwamanda Ahmed Tijjani Baba Gamawa, aikin sojojin ruwa ne su kula duk wani abu dake faruwa ta cikin ruwa, wanda kuma ya hada da matsalar da ake samu a yankin Niger Delta inda ake fasa bututun mai ana kuma satar danyen Mai.

Hakan yasa shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari, yayi aniyar kara musu karfi ta hanyar samarwa rundunar jiragen zamani don samar da tsaro ga jiragen dake sintiri ta kan ruwan kasar.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00

XS
SM
MD
LG