Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Sabon Kakaki


Birgediya Sani Usman Kukasheka
Birgediya Sani Usman Kukasheka

A wani cigaba, rundunar sojin Najeriya ta nada Birgediya-Janar JTE Chuckwu sabon Jami'in Yada Labaranta, a yayin da ta tura wanda ya gada, wato Sani Usman Kukasheka karatu a Cibiyar Koyar da dabarun shugabanci ta NIPSS, Kuru, Jos.

A wata sanarwa da kakaki mai barin gado ya fitar, Burgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya bayyana cewa za a tura shi karin ilimi a cibiyar tsare-tsare da sanin dubarun mulki ta NIPSS da ke Kuru Jihar Jos.

Bisa wannan dalilin ne za a mika ragama da kuma karbata a hukumance tsakannin sabon kakakin rundanar sojin, Birgediya Janar JTE Chukwu da tsohon kakakin Burgediya Kukasheka a ranar Litinin 26 ga watan Fabrairun 2018.

Ga sanarwar da ya yi a shafin Twitter na Rundunar Sojin Najeriya

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG