Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Shugaban Kasa Zuwa Adamawa Ta Bar Baya Da Kura


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Yanzu haka dai an soma maida martani da tsokaci game da ziyarce ziyarcen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kaiwa jihohi lamarin da ake dangantawa da batuN siyasar dubu biyu da goma sha tara.

Cikin kwanakin nan dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara wasu jihohin kasar,biyo bayan gaisuwar girma da wasu gwamnoni suka kai masa a Abuja,da kuma mahaifarsa Daura,lamarin da masu fashin baki ke ganin da walakin,wai goro a miya,kasancewar akwai wasu jihohin da aka samu tashe tashen hankula,da aka yi tsammanin shugaban zai kai jaje,amma kawo yanzu babu labarin hakan.

Manazarta da masu fashin baki na danganta irin wadannan ziyarce ziyarcen da batun zaben shekarar 2019 da kuma yunkurin tazarce, domin samun tabarrukin Sak,kamar yadda ya faru a zaben shekarar 2015.

Alal misali baya ga jihar Kano,shugaba Buhari ya kai ziyara jihar Adamawa,don bude taro kan yaki da cin hanci da rashawa,to amma kuwa sai wasu batutuwa suka biyo baya.

Mallam Muhammad Ismail dan jarida,kuma masani kan harkar siyasa ya danganta lamarin da kamun kafa,da yace gwamnoni na yi.

Shima,Alhaji Suleiman Muhammad Jada,dake goyon bayan Buhari,na ganin da kamar wuya sake kada –gangan tazarcen Sak.

Yayin dai ziyarar Buhari Adamawa,sakataren gwamnatin Adamawa Dr Umar Bindir ya jan gwalota ,inda ya bayyana cewa tun da aka kafa jihar Adamawa ba’a samu gwamna kamar Bindow ba,inda ma ya yi shaguben cewa kafin zuwan gwamnatin APC,mashunan hawa na keke NAPEP,guda goma ne kacal ke aiki a jihar biyar a Jimeta,biyar a Yola,kana biyar kuma na wajen gyara,batun da ya jawo cece-kuce.

To ko me sakataren gwamnatin ke nufi?

Ko ma da menene dai yanzu za’a ci gaba da zura ido aga tasirin irin wannan ziyara ta shugaban kasa a jihohi.

A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz domin karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG