Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Rikici Tsakanin Tibi da Fulani Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Biyar


Gwamnan Taraba Darius Dickson Isyaku
Gwamnan Taraba Darius Dickson Isyaku

Yanzu haka hankula sun kwanta a yankin Dan Anacha na jihar Taraba,biyo bayan tashin hankalin da aka samu a tsakanin wasu yan kabilar Tibi da kuma wasu Fulani da ke yankin game da takaddamar filin noma.

Kamar yadda rahotanni da kuma shaidun gani da ido suka tabbatar sabon fada ne ya kaure a yankin Dan Anacha na karamar hukumar Gassol,a tsakanin wasu yan kabilar Tibi da kuma wasu Fulani a yankin wanda ya jawo asarar rayuka a tsakanin bangarorin biyu.

Bayanai na cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon takaddama kan wani fili da kowane bangare ke ikirarin cewa na shi ne, kuma kawo yanzu an tura jami’an tsaro domin maido da doka da oda.

Rundunan yan sandan jihar Taraban ta tabbatar da mutuwar mutum biyar, baya kuma ga wadanda aka raunata. ASP David Misal kakakin rundunan yan sandan jihar, ya ce Fulani ne suka yi fashi a wani fili da Tibi suka ce nasu ne na gado saboda haka suka feshe anfanin Fulanin. Daga nan ne rikici ya barke suka soma kashe juna.

Yayinda Tibi suka shiga daji suna kai hari kan kowa suka gani, su ma Fulanin suna tare motoci a hanya suna kai sara

A cewar kakakin ‘yan sandan jihar ASP David Misal tuni har an cafke wasu da ake zargin suna da hannu a wannan aika aikan.

Jihar Taraba jiha ce dake da yawan kabilu da wajen noma da kiwon da ka iya kai jihar gaba, in ba don tashin hankalin da ake samu ba,kamar yadda masu fashin baki ke cewa.

A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG