Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kunar Bakin Wake Sun Gamu da Ajalinsu


Motar kunar bakin wake.

Rahotanni daga jihar Gombe sun ce wasu mutane da ake zaton yan knar bakin wake ne sun gamu da ajalinsu akan hanyarsu ta zuwa Bajoga.

Mutanen su uku a cikin mota suna dauke da bama bamai da shinkafa zasu shiga Bajoga a jihar Gombe.

Sun kusa da inda sojoji ke binciken ababen hawa sai bama-baman dake cikin motarsu suka tashi na take kuma ya hallakasu kafin ma su je su hallaka wasu.

Wasu da aka yi fira dasu sun ce fashewar ta faru ne kusa da sojoji dake lura da zirga-zirgan mutane kan hanyar da ta ratsa garin Bajoga ta kuma bulla jihar Yobe. Shugaban kungiyar agaji ta Red Cross yace kodayake yana Yola akan hanyarsa ta komawa Gombe daga Kamaru yaji abun da ya faru. 'Yan kunar bakin wake ne su uku amma Allah ya kiyaye kaikayi ya koma kan mashekiya. Aniyarsu ta bisu.

Su ma mazauna garin Bajoga sun yi karin bayani. 'Yan kunar bakin waken sun fito ne daga hanyar Potiskum . Shirin da 'yan kunar bakin waken suka yi ya kare a kansu.

Ga rahoton Abdullwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG