Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shugaban Amurka Zai Dankawa Manyan 'Ya'yansa Ukku Harkokin Kasuwancinsa


'Ya'yan shugaban Amurka mai jiran gado daga hagu Eric Trump da Donald Trump Jr da Ivanka Trump

A halin yanzu kuma...masana sunce daya daga cikin matsalolin da sabon shugaban Amurka din, Donald Trump zai fuskanta, shine yadda zai iya zame hannunsa daga harakokinsa na kasuwanci bayan ya dare kan karagar mulki, abinda ake ganin zai yi mishi wuya saboda sabo.

Trump, 70, yace yana son ya mika aikin gudanarda harakokinsa na kasuwanci ga manyan ‘ya’yansa guda ukku – Donald Trump Jr., Eric da Ivanka - don ya nuna cewa yana aiki da dokokin da suka haramtawa shugaban kasa raba hankalinsa tsakanin mulki da wasu hidimomi na kashin kansa.

Sai dai dokokin sun nemi ya hannunta harakokin kasuwancin nasa ga wani gungun mutane da basa da alakar jini da shi, wadanda kuma zasu iya aiwatarda duk abinda suka ga dama ba tareda sun sanar da shi ba.

Wasu masana na ganin cewa zaman Trump shugaban Amurka zai iya yin tasiri wajen bunkasa harakokinsa na kasuwanci, wanda kuma zai iya janyo cece-kucce daga wasu bangarori na masu fada-a-ji a Amurka.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG